Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

DSS ta musanta kama alkalin daya yanke hukuncin zaben gwamna a Kano

Published

on

Hukumar tsaro ta farin kaya DSS a Nijeriya ta musanta rahotannin dake cewa jami’anta sun kama guda daga cikin alkalan da suka yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano na 2023.

Wannan na zuwa ne bayan wani zargi da sakataren yada labaran gwamnan Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa yayi, cewa gwamnatin Kano na da yakinin alkalan da suka yanke hukuncin zaben gwamnan jihar, jami’an tsaro sun gayyace su tare da tsare su.

Da yake musanta zargin yayin tattaunawarsa da jaridar PR-Nigeria, kakakin hukumar ta DSS Peter Afunanya, ya musanta zargin da sakataren yada labaran gwamnan Kano Sunusi Bature Dawakin Tofa yayi cewa an kama alkalan kotun sauraran kararrakin zaben jihar.

Rahoton: Abdulkadir Kiyawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!