Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisar dokokin Kano ta amince da ƙarin sabbin kwamishinoni 4

Published

on

A zamanta na yau Talata, majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin shugabanta Alhaji Jibril Isma’il Falgore, ta tantance tare da amincewada nadin sabbin kwamishinoni guda 4 da gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata.


Kwamishinoni hudun da majalisar ta amince da nadin nasu sun hada da Adamu Aliyu Kibiya da Abduljabbar Umar Garko da Shehu Sule Aliyu Ƙaraye da kuma Mustapha Rabi’u Musa Kwankwaso, inda mambobin zauren suka sahale nadin jim kadan bayan kammala tantance su.


A nasa bangaren, shugaban masu rinjaye na majalisar kuma wakilin Dala Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa, ya bayyaana cewa dukkansu sun cancanta sakamakon nagartar da suke da ita.

Haka kuma ya ƙara da cewa, “Kundin tsarin mulkin Nijeriya ne ya yi tanadin cewa duk wanda za a naɗa a matsayin kwamishina sai ya zo mun tantance shi domin tabbatar da cancantarsa.

A ganawarsu da manema labaran majalisar, wasu cikin wadanda aka amince da nada su a matsayin kwamishinoni kuma wakilai a majalisar zartaswar jiha, sun bayyana cewa, za su zage damtse wajen ganin cewa sun bayar da gudunmawa wajen ciyar da jihar Kano gaba.

A dai zaman na yau, kudurin kafa hukumar dakile cutuka masu yaduwa ta jihar Kano ya tsallake karatu na biyu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!