Labarai
Za mu yi aiki da AOWD don tallafa wa al’umma- Gwamnatin Kano
Gwamnatin jihar Kano, ta ce za ta yi aiki ka faɗa da kafaɗa haɗa da ƙungiyar Alkhairi Orphanage and Women Development domin ci gaba da tallafa wa mutane masu buƙata ta musamman da marasa ƙarfi har ma da iyaye mata.
Kwamishinar ma’aikatar jin ƙai da daƙile talauci ta jihar Kano Hajiya Amina Abdullahi Sani, wadda aka fi sani sa Sai Mama, ce ta bayyana hakan yau Juma’a yayin da ta karɓi baƙuncin tawagar ƙungiyar yayin da suka kai mata ziyara a ofishinta.
Kwamishinar ta ce, za ta yi aiki kafada da kafada da ƙungiyar domin tallafawa al’umma musamman ta fuskar bayar da tallafi kamar yadda gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf ta saba.
“Daga manufofi da aikace-aikace da wannan ƙungiya ta gabatar mun, na tabbatar da cewa aiki iri ɗaya muke yi, don haka za mu yi aiki da ita don tallafa wa al’umma”.
A lokuta da dama muna yin aiki da irin waɗannan ƙungiyoyi inda muke basu aikin ci gaban al’umma da suke taya mu yi musamman abinda da ya shafi rabon kayan tallafi,” inji Kwamishinar.
A nata ɓangaren shugabar ƙungiyar ta Alkhairi Orphanage and Women Development Kwamared Ruƙayya Abdurrahman, cewa ta yi sun kai ziyarar ne domin neman ƙulla alaka da ma’aikatar domin ci gaban al’umma.
Ta kuma ce, ” Haka kuma mun kawo mata takardar taya murna bisa wannan sauyi data samu na muƙamin Kwamishinar ma’aikatar jin ƙai da daƙile talauci wanda muke ganin hakan babban ci gaba a gareta da ma jiha baki ɗaya.”
Kwamared Ruƙayya Abdurrahman, ta ce, aikace ƙungiyar sun hada da wayar da kan al’ummar kan muhimmancin yin awo ga mata masu juna biyu da shayar da jarirai zallar Nonon uwa da daƙile matsalar cin zarafin mata da mayar da marayu da Ƴaƴan marasa karfi makaranta da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login