Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kiris ya rage gwamnatin Buhari a kawo karshen Tsaro – Bashir Muhammad

Published

on

Kungiyar yan takarar jam’iyyar APC ta kasa reshen jihar Kano ta ce nan gaba kadan gwamnatin shugaba Buhari zata kawo karshen matsalar tsaro da ya addabi sassan kasar nan.

Shugaban kungiyar Alhaji Bashir Muhammad ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

Alhaji Bashir ya kara da cewa hakkin gwamnati ne samar da tsaro da kare dukiyar al’umma, sai dai ya ce al’umma ma na da gagarumar rawar da zasu taka wajen inganta tsaro musamman waje bayar da bayanan sirri tare da aiki Kafada da Kafada da jami’an tsaro don kawo karshen matsalar.

Ya kuma jaddada cewa gwamnatin shugaba Buhari za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa al’umma don kawar da fatara da kuma samar da ayyukan yi ga jama’a.

Bashir Muhammad, ya yi kira ga al’umma da su dauki gabarar kishin Kasa tare da cire Kabilanci da bangaranci a zamantakewarsu wanda hakan zai taimaka wajen magance fadace-fadace da zubar da jinin al’ummar kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!