Labarai
Jami’an KAROTA sun karbi horon bada agajin gaggawa

Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, ta ce za ta fara yin amfani da sababbin dabarun zamani wajen fannin bayar da agajin gaggawa.
Shugaban hukumar Injiniya Faisal Mahmud Kabir, ne ya bayyana hakan a wajen taron bayar da horo kan dabarun bayar da agajin gaggawa ga jami’an hukumar ta hadin gwaiwa da sashen nazarin halayyar dan-Adam na jami’ar Bayero suka shirya.
A nata bangaren, Malama Rahama Sulaiman da ta kasance guda cikin masu bayar da horon ta ce, horon da jami’an na KAROTA suka samu zai kawo sauki wajen taimaka wa mutane da kuma gudanar da ayyukan hukumar.
Haka kuma, ta bukaci jami’an hukumar da suka samu horon da su yi amfani da shi ta hanyar da ta dace domin ceton rayukan al’umma a lokacin da wani iftila’i ya faru.
You must be logged in to post a comment Login