Labarai
INEC ta bada shaidar lashe zabe ga sabbin yan majalisar dokokin Kano 2

Hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC shityyar Kano, ta mika shaidar lashe zabe ga yan majalisun jihar Kano da na kananan hukumomin Bagwai da Shanono da kuma Ghari da Tsanyawa wadanda suka lashe zaben da ta gudanar.
Hukumar ta mika shaidar ne a shalkwatar ta dake nan Kana a yau Juma.
Yan majalisun hadar da Ali Lawan Alhassan daya fito daga kananan hukumomin Bagwai da Shanono daga Jam’iyyar ANPP sai Garba Yau Gwarmai daga karamar hukumar Ghari da Tsanyawa daga Jam’iyyar APC.
Da yake jawabi shugaban hukumar ta INEC a nan Kano Ambasada Abdu A. Zango ya ce, yanzu sun kammala kowanne zabe a Kano dan haka yake kara kira ga al’umma da suje suyi Rijistar zabe ga wadan da basu da ita.
A nasa jawabin Ali Lawan Alhassan daga kananan hukumomin Bagwai da Shanono ya bayyana jin dadinsa tare da kudirin gudanar da ayyuka a yankin nasa.
Shi kuwa Garba Yau Gwarma na kanann hukumomin Ghari da Tsanyawa cewa yai zai dora kan ayyukan da ya ke yi a baya yayin da ya ke wakiltar mazabar tasa a baya.
Taron bada shaidar cin zaben dai, ya samu halartar shugabannin hukumar ta INEC da na Jam’iyyar APC har ma da wasu daga Jam’iyyar NNPP.
You must be logged in to post a comment Login