Labarai
An yi zangazangar kin amincewa da kara masarautu a Kano
Mambobin wata kungiya mai rajin kishin al’ummar Kano da wasu daga cikin mutanen jihar Kano sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawa da sanya hannun da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya yi kan dokar kara kirkirar Masarautu 4 a jihar Kano.
Shugaban kungiyar mai suna Kano First Forum, da mutanen da suka gudanar da zanga-zangar sun fara ne daga shataletalen Gidan murtala da ke tsakiyar birnin Kano da tsakar ranar yau Alhamis.
Masu zanga-zangar dai sun tsaya ne a bakin titi dauke da Kwalaye dauke da rubutu daban-daban da ke nuna rashin amincewa da sanya hannun da gwamnan Kano ya yi a jiya Laraba kan dokar, a kokarin su na yin tattaki zuwa majalisar dokoki ta jihar Kano.
Sai dai kokarin jin ta bakin shugabana kungiyar Dr Yusuf Ishaq Rabi’u ya ci tura sakamakon cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gayyace shi zuwa shalkwatarta da ke unguwar Bompai a nan Kano.
Jami’an ‘yan sandan dai sun tare masu zanga-zangar a bakin ofishin hukumar kashe gobara ta jihar Kano tare da hana su zuwa zauren majalisar dokokin ta jihar Kano.