Kiwon Lafiya
Lauya mai fafutukar kare hakkin bil adama ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban kasa
lauyan mai fafutukar kare hakkin bil’Adama Femi Falana ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wata takarda da ya ke bukatar a saki wasu wasu mutane 40 da rundunar ‘sojin ruwan kasar nan ta kama ba bisa ka’ida ba.
Ta cikin takardar mai dauke da kwanan watan 19 ga watan Mayun da muke ciki, Falana ya ce an samu korafe-korafe daga iyalan wadanda aka kama din, la’akari da yadda aka chafke su ba tare da gurfanar da su karkashin umarnin hukumomin runar sojin ruwan ba.
Falana ya kuma kara da cewa kame mutanen tare da tsare sun a kimanin watanni 6 ba tare da gurafanar da su ba, take hakkin bil’adam ne.
Lauyan ya kuma ce ya rubuta wannan wasika ne la’akari da yadda aka rike mutanen na watanni 6 tare da cin zarafin su wanda hakan yin fatali da hakkin da doka ta basu ne karkashin sashen na 34 da 35 na kundin tsarin mulkin kasara nan.
Ya ce hakan na nuna yadda gwamnatin tarayya bata damu da hakkin al’ummar kasar nan ba, kuma ya zama dole shugaban kasa Muhammadu Buhariy a dakatar da hafsan sojin saman kasar nan.