Labarai
Shalkwatar tsaro zata bayyana bincike badalakar tserewa da kudade naira miliyan 400
Shalkwatar tsaro ta kasa ta ce, za ta bayyana wa al’ummar kasar nan sakamakon binciken da za ta gudanar game da badakalar tserewa da kudade da suka kai naira miliyan dari hudu da wasu sojoji su ka yi, wanda ake zargin kwamandan shiyya ta takwas da ke Sokoto Manjo Janar Hakeem Otiki da hannu cikin lamarin.
Mai rikon mukamin daraktan yada labarai na shalkwatar tsaro ta kasa, kanal Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka, yayin wani taron manema labarai jiya, a Abuja.
Ya ce, tuni bincke ta yi nisa kan batun, kuma da zaran an kammala za a sanar da al’ummar kasar nan sakamakon sa.
A baya-bayan nan ne dai, rahotanni su ka bayyana cewa, tuni rundunar sojin kasar nan ta kama tsohon babban kwamandan shiyya ta takwas da ke Sokoto, Manjo Janar Hakeem Otiki, bayan tserewa da wasu sojoji da ke rakiyar kudaden da aka ce, shi ya aikesu da shi zuwa garin Kaduna.
Sojojin da su ka tsere da kudaden wadanda rahotanni su ka ce ba a san ko daga ina aka samosu ba, sun hada da: Corporal Gabriel Oluwaniyi da Corporal Muhammed Aminu da Corporal Haruna da Oluji Joshua da kuma Hayatuddeen.