Connect with us

Labarai

Sojoji sun hallaka ‘yan Boko Haram 17 a Borno

Published

on

Dakarun Operation Lafiya Dole na Rundunar Sojin kasar nan sun kashe ‘yan boko haram guda goma sha bakwai akan titin Damboa zuwa Maiduguri a jihar Borno.

Hakan na cikin wata sanarwa ce mai dauke da sa hannun mai magana da yawun shalkwatar tsaro ta kasa, Manjo Janar John Enenche.

Sanarwar ta ce, dakarun bataliya ta ashirin da biyar da ke aiki a garin Damboa tare da hadin gwiwar dakaru na musamman, sune su ka yi kwanton bauna ga ‘yan boko haram din tare da hallaka wasu da dama.

A cewar sanarwar bayan gumurzu na ‘yan mintuna sojojin sun kashe ‘yan ta’addar guda goma sha bakwai, yayin da wasu da dama suka tsere da raunuka a jikinsu.

Sai dai, wasu sojoji guda biyu sun rasa rayukansu yayin da wasu guda hudu suka jakkata a yayin fafatawar, a cewar sanarwar.

Yanzu haka dai tuni kwamandan dakarun Operation lafiya Dole ya ba da umarnin kara turawa da dakaru na musamman domin gudanar da ayyukan tsaro akan titin da ya hada garuruwan Damboa da Maiduguri.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!