Labarai
PRP zata daukaka kara kan hukuncin kotu ta yanke na sanata Uba Sani na jami’yyar APC
Jam’iyyar PRP ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin da kotun sauraran korafin zaben ‘yan majalisun dokokin tarayya na jihar Kaduna ta yanke game da kalubalantar nasarar da Sanata Uba Sani na jam’iyyar APC ya samu a yayin zaben da ya gabata.
A cewar jam’iyyar ta PRP ba ta gamsu da hukuncin da kotun ta yanke ba, a don haka za ta kalubalanci Matakin a kotu na gaba.
Da ya ke zantawa da manema labarai shugaban jam’iyyar a jihar ta Kaduna Alhaji Abdurrahman DanRimi, ya bayyana hukuncin a matsayin abin kunya wanda kuma jam’iyyar ba za ta amince da shi ba.
Tun farko dai kotun karkashin jagorancin mai shari’a A.H Suleiman a jiya Laraba ta yi watsi da korafin da Sanata Shehu Sani na jam’iyyar PRP ya shigar gabanta.
Kotun ta ce Sanata Shehu Sani ya gaza gamsar da ita cikakkun hujjojin da za su sa soke zaben.