Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotun daukaka kara a Abuja ta tabbatar da nasarar Abdullahi Sule a Nasarawa

Published

on

Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da nasarar zaɓen gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa.

 

A hukuncin da kotun ta yanke yau Alhamis, alƙalan kotun sun bayyana cewa, kotun sauraron ƙorafin zaɓen gwamnan jihar Nasarawa ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke.

 

A watan da ya gabata ne dai kotun sauraron ƙorafin zaɓen jihar Nassarawa ta soke nasarar gwamna Abdullahi Sule na jam’iyyar APC, tare da bayyana David Ombugadu na PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen na watan Maris ɗin 2023.

 

Tun farko, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya, INEC, a sakamakon zaɓen gwamnan jihar ta ce Abdullahi Sule na APC ya samu ƙuri’a 347,209, inda ta ce ya doke Ombugadu na PDP, wanda ya samu ƙuri’a 283,016

 

 

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!