Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Amarya ta haihu bayan wata hudu da Aure

Published

on

Wata mai jego Maryam Bilal da madaurin auren ta Musa Khalil sun gurfana a gaban kotun majistratrate mai lamba 62, dake zaman ta a garin Minjibir, karkashin mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, da tuhumar hada kai da aikata laifi da kuma cutarwa laifukan da suka saba da sashi na cashi’in da bakwai da kuma na dari uku da ashirin da biyu, na kundin tafikadda shari’ar musulunci na jihar Kano.

Wani mutum ne dai Aminu Ibrahim, ya yi karar su a ofishin yan sanda na Minjibir cewar Musa Khalil din ya aura masa Maryam alhalin tana dauke da juna biyu, kuma watan ta hudu da kwana ashirin da takwas ta haihu.

Koda Dan sanda mai gabatar da kara sajan Kabiru Bashir ya karanta musu kunshin tuhumar da ake musu, sai suka musunta. A nan ne mai shari’ah Ibrahim Sarki Ibrahim, ya daga zaman zuwa ranar sha hudu ga wannan watan da mu ke ciki Dan cigaba.

Daga nan ne Lauyan da yake kare su ya roki kotun da ta sanya su a hannun beli. Kuma kotun ta amince da rokon ta kuma sanya su a hannun belin, bisa sharadin mutane biyu masu kamala su tsaya musu sannan kuma su bada hotunan su na passport guda biyu a kotun sannan kuma dan sandan kotun ya je ya gano gidajen su. In kuma wadanda akai belin suka tserewa shari’ah masu belin za su bada duba dari dari.

Kuma bayan an fito daga kotun Maryam din ta shaidawa wakilin mu Abubakar sabo cewa wani ne mai suna Sunusi Bala alale ya yi mata.

Shi ma madaurin auren na ta Musa Khalil ya magantu.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!