Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Da Dumi-dumi: Kotu ta hana jami’an tsaro fitar da Sarki Sanusi Lamido daga Fadarsa

Published

on

Wata babbar kotun jihar Kano karkashin jagorancin mai shari’ah Amina Aliyu, ta umarci hukumomin tsaro da su kauce wa duk wani yunkuri na fitar da Mai Martaba Sakin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadarsa.

Kotun ta bayyana hakan ne ta cikin wani umarni da ta bayar a yau Talata.

ta cikin umarnin kotun ta umarci jami’an yan sanda da na hukumar DSS har ma sojoji da sauran jami’an tsaro da su kauce wa wannan yunkuri.

Umarnin kotun ya biyo bayan karar da Mai Martaba Sarkin ya shigar gabanta hadin gwiwar masu nada sarki hudu da suka hadar da Madakin Kano Yusuf Nabahani da Makaman Kano Ibrahim Sarki Abdullahi da Sarkin Bai Mansur Adnan da Kuma Sarkin Dawaki mai tuta Bello Tuta.

Da take bada umarnin, mai shari’ah Amina Aliyu ta haramta wa hukumomin tsaron kamawa ko cin zarafin sarkin har ma da mutanen hudu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!