Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Gwamanti ta kebe fiye da bilyan goma don noman rani a Kano -Sani Bala

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan sha hudu domin inganta noman rani a jahar Kano, a yankunan kananan hukumomin Kunci da Tsanyawa.

Danmajalisar wakilai mai wakiltar yankunan injiniya Sani Bala Tsanyawa ne ya bayyana haka a wata tattaunawa ta musamman da yayi da Freedom Radio.

Injiniya Sani Bala Tsanyawa yace idan aka kammala aikin za’a iya noma kadada fiye da dubu ashirin n a yankin.

Yace idan har za’a noma kadada fiye da dubu ashirin zai habaka tattalin arzikin yankin na Kunci da Tsanyawa da kuma jahar Kano gaba daya.

‘’Noman rani na da muhimmanci kwarai da gaske wanda idan aka kammala shi zai taimaka wajen inganta aikin gona da’’ inji Injiniya Sani Bala.

Danmajalisar wakilan ya kara da cewa dalilan siyasa ne ya saka aka dakatar da aikin inganta noman rani na yankin.

‘’An amince da kusan Naira biliyan hudu zamanin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke shugaban hukumar asusun rarar man fetur ta PTF ,amma ba’a karasa ba ,dalilan siyasa yasa aka dakatar zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo’’

 

Akwai kuma wani aikin madatsar  ruwa ta ‘’Yanganau wanda a yanzu an ware miliyan hamsin a yankin domin karasawa  da inganta aikin.

A yanzu babu wata Sana’a da zata yi maganin rashin aikin yi da ya wuce noman rani, wanda yace akwai wasu mutane na yankin arewacin Kano da suke barin jahar Kano zuwa wasu yankuna domin gabatar da noman rani.

Yace akwai wasu al’aummar yankin na Kunci da Tsanyawa da Kunci dake zuwa jihohin Niger da Nasarawa domin noman rani amma a yanzu za su dara.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!