Manyan Labarai
Jagorancin siyasar birnin Kano: Sha’aban Sharada ko Mukhtar Ishaq Yakasai?
Tun lokacin da aka kammala zaben shekarar bana a fadin tarayyar Najeriya ,hankula suka ta’allaka ga mutanen da suka lashe zabe a kowanne mataki, kama daga shugaban kasa ,majlisun tarayya da na jihohi da kuma gwamnoni.
Jahar Kano na daya daga cikin jihohin tarayyar Najeriya da harkokin siyasar jihar ke daukar hankali a fannoni da dama , wannan daukar hankali da siyasar jahar Kano ke yi ta saka wasu ke sha’awar siyasar ta jahar Kano da kuma alhini da hakan ke haifarwa ga zukatan wasu al’umma.
Kwaryar birnin Kano dake da tsohon tarihi na al’adu da saurata ,haka ma siyasar wannan birni take, tsakiyar birnin na Kano da kewaye na taka rawa wajen wanda zai lashe zaben gwamnan jahar Kano tun daga lokacin da aka fara tsarin tarayya a Najeriya wanda ya bayar da damar zaben gwamnoni a sauran jihohin tarayyar kasar nan.
Tun dawowa mulkin dumokradiyya da Najeriya tayi a shekarar 1999, siyasar kwaryar birnin Kano ke jan hankali matuka, kwaryar birnin ta Kano da ake kira da Kano Municipal council, nan ne guri da abubuwa da dama ke zagayawa da ya shafi siyasa.
Yayin da zaben shekarar 2019 ya karato jam’iyya mai mulkin jahar Kano wato APC ta gabatar da zaben fitar da gwani da ya fara daga ‘‘yan takarar gwamna har zuwa sauran ‘’yan takara.
Wadannan ‘’yan takara su ne ,na majalisun dattijai da na wakilai da na jihohi.
An samu canjin sunaye na ‘’yan takarar da tun usuli suka lashe zaben fitar da gwani a jam’iyyar APC a fadin jahar ta Kano.
Tunda muna magana ne akan karamar hukumar birnin Kano, wannnan karamar hukuma na daya daga cikin kananan hukumomi a jahar da siyasar su take da wahalar gudanarwa.
Misali ,shi ne tsohon kakakin majalisar wakilai ta tarayyar Najeriya, Ghali Umar Na’abba, sai da ya fadi zabe a yankin karamar hukumar ta birni a zaben shekarar 2003, wannan ya nuna irin tataburzar da siyasar ta tsakiyar birnin na Kano ke da shi.
Kafin gudanar da zaben majalisun dokoki na tarayyyar Najeriya , an ayyana tsohon mai taimakawa shugaban Najeriya a harkokin yada labarai Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin dantakarar majalisar wakilai ta tarayya .
Hakan ta saka sabon kwamishinan ayyuka na musamman na jahar ta Kano Mukhtar ishaq Yakasai yakai kara gaban babbar kotun tarayya dake nan Kano inda tace shi Mukhtar Yakasai ne halatttacen dantakarar da jami’yyar ta APC ta tsayar.
Ana haka ne ,shi ma Shaaban Ibrahim Sharada ya daukaka kara zuwa kotun daukaka kara inda ita kuma tace shi ne dantakar.
Mukhatar Ishaq Yakasai shi ma ya daukaka kara zuwa kotun kolin tarayyar Najeriya .
A haka dai aka tafi zaben majalisun tarayya wanda daga baya kotun daukaka kara ta tabbatar da Shaaban Ibrahim sharada a matsayin dantakarar majalisar wakilai,.
Hukumar zabe ta ba shi takardar shaidar zama halattacen danmajalisar wakilai daga yankin birnin Kano.
Bayan rantsar da yan majalisun dokokin ta tarayyar Najeriya , sai ga shi Sha’aban Ibarahim Sharada ya zama shugaban kwamitin kula da tsaro na majalisar ta wakilai.
Kwatsam sai ga shi ‘’yan siyasa magoya bayan ‘’yan siyasun biyu anan birnin Kano na shiga kafafan yada labarai suna musayar yawu akan waye yake da hakkin shugabancin siyasar ta birnin Kano.
Daya daga cikin tsofaffain ‘’yan siyasa da suka fito daga birnin na kano kuma ‘’yan jamiyyar APC kamar su Alhaji Hamza Darma suna ganin Honourable Shaaban Ibrahim Sharada ne jagoran siyasar birnin na Kano ,tunda shi ne yake rike da babbar kujera daga karamar hukumar .
Bayan Alhaji Hamza Darma a kwai wasu ‘’yan siyasun da dama da suke ganin Sha’aban Ibrahim Sharada a matsayin shugaban siyasar birni.
Duk da haka wasu daga cikin magoya bayan shugaba Buhari da suka fito daga karamar hukumar birnin suna ganin bai kamata ace Sha’aban Ibrahim Sharada ne jagoran siyasar babbar karamar hukuma irin ta birnin Kano ba.
Shin wannan dalili ne ya saka wasu ke ganin sha’aban Ibrahim Sharad bai cancanci ya zama jagoran siyasar karamar hukumar birni ba ,ko dan suna ganin shi matashi ne ?
Idan kuma saboda matashi ne to ai yana rike da kujerar majalisar wakilai ta wajen.
Ko menene ya saka wasu a karamar hukumar ta birni ke ganin lallai sai sabon kwamishinan ayyuka na musamman ne zai zama jagoran na siyasar birni, sai dais hi Mukhtar Ishaq Yakasai a yanzu ba zababbe ba ne , nadadde ne.
Da nadadde da zababbe wa ya kamata ya jagoranci al’umma.
Masana fashin baki na siyasa na ganin cewa duk al’ummar da ta zabi mutum ya wakilce ta, to za ta iya ba shi jagoranci.
Lokaci ne kawai , zai tabbatar da hakan.