Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Gwamnatin Kano zata fara aiwatar da tsarin asusu bai daya a shekara ta 2020

Published

on

Asusun bai-daya

Gwamnatin Kano ta ayyana watan Junairun shekara ta 2020 a matsayin lokacin da zata fara aiwatar da tsarin asusun bai daya na gwamnatin jihar Kano wato TSA

Babban sakataren ma’aikatar kudi zakari Sadiq Buda ne ya bayyana haka a jiya litinin yayin taron karawa juna sani ga daraktocin gudanarwa na hukumomin gwamnati da akantoci ma’aikatu daban daban.

Mal Buda wanda ya sami wakilcin kwamishin kudi , Shehu Na Allah Kura wanda ya ce wannan tsari na daga cikin hukuncin da suka yanke a wajen wata tattaunawa da hukumomin gudanarwa ma’aikatun gwamnati a taron da aka yi a watan Nuwamban shekara ta 2017.

Ya ce gwamnatin jiha ta bada kwangilar sanya wata manhajjar da zata taimakawa yiwuwar aikin ga ma’aikatun gwamnati jiha, domin su aiwatar da shi.

Da ya ke Magana wanda ya ke kula da shirin sanya manhajjar , Seth David Gana  ya ce horon zai taimaka musu wajen amfani wannan manhajjar.

Mal Gana ya ce tsarin  asusun guda na gwamnati zai taimaka inganta tsarin wajen tabbatar da gaskiya da adalci a yadda take kashe kudadenta.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!