Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalibai 30 ne suka koyi sana’o’in dogaro da kai a Wudil

Published

on

A yau Lahadi ne makarantar al’umma ta Bahaz Integrated Academy dake garin Wudil a nan Kano ta yaye dalibai guda talatin 30 da sukaci gajiyar koyon sana’o’in dogaro da kai.

Daliban da aka yaye sun samu koyon sana’ar dinki da makarantar ta shirya, Inda aka raba musu takardun shaidar koyo da kuma kyaututtuka.

Yayin da wasu daliban ke karbar takardar shaida.

Da yake jawabinsa a yayin taron shugaban makarantar Malam Bilyaminu Usman Usman ya bayyana cewa ba komai ne ya sanya su yin wannan aiki ba sai kokarin samarwa da al’umma ayyukan yi, domin magance zaman banza.

Shugaban makarantar Malam Bilyaminu Usman Usman yayin da yake jawabi.

Malam Bilyaminu ya kara da cewa daga cikin abubuwan da suke koyarwa ga daliban makarantar sun hadar da hada Takalmi, Jaka, Kiwon Kifi da Kiwon Kaji da kuma koyar da amfani da na’ura mai kwakwalwa wato Kwamfiyuta.

Kakakin rundunar’yan sanda ta jihar Kano, da shugaban karamar hukumar Wudil a wurin taron.

Su ma wasu daga cikin daliban da suka amfana da koyarwar sun shaidawa Freedom Radio farin cikin su, tare da godiyarsu ga hukumar makarantar.

Daga cikin mahalarta taron sun hada da wakilin kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, wanda kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya wakilta, da shugaban karamar hukumar ta Wudil Mallam Saleh Kausani da sauran iyayen yara da al’ummar garin ta Wudil.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!