Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Kar wanda ya kara biyan haraji ga ma’aikatanmu- Hukumar tattatara kudin shiga ta jiha

Published

on

Shugaban hukumar tattara kudaden shiga ta Kano

Hukumar tattara kudaden shiga   ta jihar Kano ta bukaci masu biyan haraji a jihar Kano da kar su ke bawa ma’aikatan hukumar kudi a matsayin hanya ta biyan haraji.

Shugaban hukumar Sani Abdulkadir Dembo ne ya bayyana haka lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.

Sani Dembo ya kara da cewa hukumar ta fito da tsare tsaren da mai biyan haraji zai bi ta banki kuma a ba shi rasiti wanda zai zame masa hujja.

Yace daga inganta hukumar zuwa yau hukumar tattara kudaden shigar ta jihar Kano na samun Naira biliyan biyu zuwa sama duk shekara.

Sani Dembo yace a  baya kafin inganta hukumar gwamnatin Kano na samun Naira miliyan dari uku zuwa sama ne kacal a matsayin kudaden shiga.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!