Connect with us

Labarai

FIRS ta kara wa’adin biyan haraji ga kamfanonin da ba su biya akan lokaci ba

Published

on

Hukumar tattara kudaden shiga ta kasa FIRS ta kara wa’adin da ta bai wa wadanda suka gaza biyan kudaden haraji na kamfanoni da sauran mutane dai-daiku har zuwa ranar 31 ga watan Agusta mai kamawa.

Shugaban hukumar Muhammad Nami ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran hukumar Abdullahi Ahmad ya fitar ranar Laraba.

Muhammad Nami ya ce wannan wani mataki ne na sauki ga jama’a da hukumar ta bijiro da shi na tallafawa masu biyan haraji, sakamakon illar da annobar cutar corona ta haddasawa al’ummar kasar nan.

To sai dai ya bayyana cewa babu wani shiri na sake tsawaita wa’adin a nan gaba, a don haka duk wanda ake bi bashin ya hanzarta biya don kaucewa fushin hukumar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!