Labaran Kano
BUK: dalibai 300 sun sami tallafin karatu
Kimanin dalibai ‘yan asalin jihar kano 300 ne suka sami tallafin karatu a jami’ar Bayero ta Kano.
Shugaban jami’ar Bayero ta Kano Farfesa Muhammad Yahuza Bello ya bayyana cewa hukumar makarantar za ta kashe kimanin naira miliyan 15 ga ‘yan asalin jihar karkashin tsarin nan na bada tallafi ga daliban da suka yi kwazo a karshen zangon karatunsu kuma suke da matsala ta kudi.
Shugaban jami’ar ya kara da cewa jami’ar ta samu daliban da suke da kwazo a gasa daban-daban da aka gudanar a jihohin Najeriya.
shugaban jami’ar ta Bayero ya kuma bada misalai da wasu dalibai 4 da suka lashe gasar Hult Prize global student da aka gudanar a Ingila, inda daliabai daga kasashe akalla 125 suka shiga gasar.
Daga cikin daliban da aka karrrama a yayin taron sun hadar da gasa a fannin wassanin.
Farfesa Muhammad Yahuza ya kuma ce jami’ar za ta cigaba da bada tallafin karatu ga dalibai masu kwazo da suke fama da matsalar kudi, domin basu damar cimma burinsu na rayuwa.
Inda yake cewa a yanzu jami’ar ta kashe kimanin naira miliyan 15 wajen tallafawa dalibai 300.
Daga cikin daliban da suka samu tallafin dai akwai AbdulHafeez Adebayo, da UbaiduRahman Suleiman da Mustapha Sani Abdullahi da kuma Olumide Gabriel.