Connect with us

Labaran Kano

Jami’ar Bayero ta yi bikin yaye dalibai karo na 35

Published

on

Jami’ar Bayero ta Kano ta bayyana aniyarta ta kara kaimi wajen samar da ingantaccen yanayin koyo da koyarwa ga dalibai.

Shugaban jami’ar Farfesa Muhammad Yahuza Bello ne ya bayyana hakan yayin bikin yaye dalibai karo na 35 da aka gudanar a dakin taron yaye dailbai dake harabar jami’ar a yau Litinin.

Ya ce daya daga cikin matakan da suka dauka wajen cimma wannan buri sun hadar da baiwa masu bukata ta musamman damar yin zarra a kwasa-kwasai daban-daban da kuma tallafawa dalibai masu karamin karfi guraben karatu da jami’ar zata rinka yi a kowace shekara.

A yayin bikin na yau dai tsangayun nazarin aikin noma da Kwamfuta da fasahar sadarwa da kuma na ilmi ne suka yaye daliban nasu da suka samu daraja daban-dabam, inda kuma tuni jami’ar ta fara sabbin kwasa-kwasai a bangaren Injiniya da manhajar Kwamfuta da kuma tsaron yanar sadarwa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 341,025 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!