Connect with us

Manyan Labarai

Siyasa: Shin ritayar da Ganduje yayiwa Kwankwaso ta tabbata?

Published

on

Jim kadan bayan kotun koli ta tabbatar da nasarar da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje  a zaben shekarar bara wasu daga cikin magoya bayan Gwamna Ganduje suka rika kai ziyarar taya murna ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A irin jawaban da gwamnan ya rika yi an rawaito  cewa Gwamnan ya ayyana ritayar siyasa da yayiwa tsohon amininsa a siyasance kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakan ya biyo bayan tataburza da gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi kafin ya koma mukamin nasa na gwamnan Kano.

Masu bibiyar al’amuran yau da kullum sun san cewar Gwamnan jihar Kano mai ci a yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sha tataburza kafin ya lashe zaben gwamna a watan Maris na shekarar ta bara.

Sai da ta kai an kai zagaye na biyu kafin a bayyana wanda ya lashe zaben gwamnan na jihar Kano.

Bayan rantsar da gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ne babban abokin karawarsa a zaben gwamnan na Kano kuma dantakarar jamiyyar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a gaban kotun sauraran kararrakin zaben gwamna yana kalubalantar ayyana gwamna Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano.

Kotun sauraran kararrakin zaben wanda mai shariah Halima Shamaki ke jagoranta ta yanke hukunci da cewa gwamna Abdullahi Ganduje ne ya lashe zaben na gwamnan Kano.

Sai da ta kai Injiniya Abba Kabir Yusuf ya kai ga kotun kolin kasar nan domin ganin ya tabbatar da an yanke hukunci, sai dai duk hukunce hukunce da kotun kasa da na kolin suka yi babu wacce ta bawa Abba Kabir nasara.

Duk da cewa ba tsohon aminin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ne ya tsaya takarar gwamna ba wato injiniya Rabiu Musa Kwankwaso sai gashi gwamna Ganduje na cewa yayiwa Kwankwaso ritaya a siyasar Najeriya.

Amma ana ganin dalilan da yasa gwamna Ganduje yace yayiwa Kwankwaso ritaya a siyasar Najeriya hakan ba zai rasa nasaba da cewa dantakarar gwamna na jamiyyar PDP Abba Kabir Yusuf jagoran jamiyyar PDP kuma tsohon Gwamna Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ne ya tsayar da shi.

Buhari ya nada Abdulrahman Baffa Yola a matsayin mai takaimakasa a harkokin siyasa

Shugaba Buhari yayi ganawar sirri da wasu tawagar yan siyasa daga Kano

Masharhanta al’amuran siyasa na ganin cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bai dauki abokin takarar sa lokacin zaben gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin barzana gare shi a siyasa ba, illa tsohon amininsa kuma tsohon gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

Hakan ba zai rasa alaka da raba gari da suka yi a siyasa ba tun bayan shi tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso ya tsayar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda zai gaje shi a zaben shekarar 2015.

Bayan gwamna Ganduje ya lashe zaben ne ,rigimar siyasa ta kunno kai a jihar ta Kano inda Gwamna Ganduje ya bar gidan siyasar Kwankwasiyya shima ya kafa gidansa wanda ake kira da Gandujiyya.

Shima tsohon gwamna Inijiniya Rabiu Musa Kwankwaso an taba rawaitowa cewa ya taba yin ikirarin zai yiwa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da shugaban kasa Muhammadu Buhari ritaya a siyasa.

Amma Gwamna Ganduje bai mayar da martani ba sai bayan fiye da shekara daya da ikirarin da aka ce tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso yayi na yiwa Gwamna Ganduje da shugaba Muhammadu Buhari ritaya a siyasar Najeriya.

Ko shin menene yin ritaya a siyasa kamar yadda ‘’yan siyasar  biyu suka rika ambatawa,wato Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso?

Idan har ritaya a siyasa shine faduwa zabe ko rasa mukami na siyasa to shi kansa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje tsohon Gwamnan Kano kuma Sanata mai wakiltar Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau ya taba yi musu ritaya a siyasa a shekarar 2003 har zuwa shekarar 2011.

Ko hukuncin Kotun Koli ya kawo karshen Siyasar Kwankwasiya a Kano?

Ko babban Akanta na Najeriya zai yi takarar Gwamnan Kano?

A tsawon shekaru takwas da Malam Ibrahim shekarau yayi yana mulkin Kano sai da aka daina jin duriyar tsohon Gwamnan Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso musamman ma tsohon mataimakinsa Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Duk da gwamnatin tarayya zamanin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ta bawa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso ministan tsaro shi kuma Dr Abdullahi Umar Ganduje ya zama mai taimaka masa na musamman yanayin siyasar Kano sai da ya juya musu baya.

Har sai a shekarar 2011 da suka sake lashe zabe a karkashin jam’iyyar PDP sannan yanayin siyasar Najeriya ya fara yi da su har zuwa yanzu.

Ko yaya wannan ritaya da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yace yayi wa Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso zata kasance ?

 

 

Manyan Labarai

Bana neman matar Aure-BABANGIDA

Published

on

Tsohon shugaban mulkin sojin kasar nan janar Ibrahim Badamasi Banagida mai ritaya, ya ce, shi kam baya neman wata matar aure.

A wata zantawa da yayi da jaridar Daily Trust, janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya, ya ce, shi ba ya bukatar yin aure a yanzu, saboda duk wata kulawa da ya kamata ‘ya’ya su yiwa mahaifinsu ‘ya’yan sa, na yi masa.

Ya ce, a yanzu  a matsayin sa na dattijo dan sama da shekaru saba’in, yana ga ba ya bukatar sai ya yi aure.

A baya-bayan nan ne dai, rahotanni su  ka yi ta yawo a kafafen yada labarai da ke cewa, tsohon shugaban mulkin sojin na neman matar aure.

A ranar 7 ga watan Disamban shekarar 2009 ne, mai dakin tsohon shugaban kasar, Hajiya Maryam Ibrahim Badamasi Babangida, ta rasu a wani asbiti da ke birnin Los Angles a jihar California da ke kasar Amurka bayan ta yi fama da cutar daji. Tun daga nan dai har ya zuwa yanzu, tsohon shugaban kasar, bai kara yin aure ba.

Continue Reading

Labaran Kano

Rashin tsarin Siyasa na gari, shi ke cutar da Kano- Dattawan Jihar Kano

Published

on

Kungiyar da ke rajin ganin cigaban  jihar Kano mai suna Kano Concern Citizen Initiative, ta ce rashin tsarin siyasa na gari shi ke dankwafe cigaban jihar Kano.

A cewar kungiyar jihar Kano ta na shan fuskantar matsaloli da dama a wannan lokaci sakamakon rashin kyakkyawar tsarin siyasa na gari wanda zai daura jihar a turba mai kyau.

Wannan dai jawabi ne da shugaban kungiyar Alhaji Bashir Usman Tofa ya yi a zantawar sa da manema labarai, bayan kammala taro kan harkokin tsaro wadda kungiyar ta shirya yau a nan Kano.

Ya ce kungiyar ta damu matuka kan irin mawuyacin hali na koma baya ta kowace bangare Wanda jihar ke fuskanta a yanzu, wanda hakan ya sa suka ga ya zama wajibi su kira taron domin nemo mafita.

A nasa bangaren dattijo Alhaji Isah Bayero ya ce dole ne Idan an tashi irin wannan taro a rika duban matsalolin da ya shafi yankin Arewa baki daya saboda halin da ake ciki a Najeriya duk abinda ya shafi jihar Kano to ya shafi Arewa baki daya saboda haka ya bukaci masu shirya taron da su fadada tunaninsu wajen ganin ci gaban yankin Arewa.

A nasa bangaren shugaban cibiyar harkokin kasuwanci ta jihar Kano Alhaji Dalhatu Abubakar ya ce akwai rashin hakuri da Kuma juriya na ‘yan kasuwar jihar Kano ya na taka rawa wajen samun koma baya a harkar kasuwanci.

A cewar sa a lokuta da dama za su samu dama ta taimaka wa Yan kasuwa amma da an kawo tsarin sai Yan Kasuwa su ki zuwa su shiga cikin tsarin, yana mai cewa burunsu kawai kullum suji ance gwamnati za ta raba kudi ga yan Kasuwa nan ne za ka gansu gaba wajen rige-rigen zuwa.

Taron ya amince cewa har sai al’ummar jihar Kano baki daya sun hada kansu sannan za a samu nasarar dakile matsalolin da ke addabar jihar.

Continue Reading

Labaran Kano

Gwamnatin Kano za ta yi rigakafi ga yara sama da miliyan 3

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce za ta ci gaba da yakar cutar shan inna wato Polio, kasancewar cuta ce da ta ke taba laka tare da haifar da shanyewar wani bangare na jikin kananan yara a cikin kankanin lokaci.

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya bayyana hakan yau a wani taron manema labarai da ya mayar da hankali a kan gangamin rigakafin cutar ta shan’inna da za a gudanar a kananan hukumomi 44 da ke nan jihar Kano.

Dakta Tsanyawa ya kuma kara da jan hankalin iyaye wajen baiwa jam’ian lafiya dake zagayawa gida-gida hadin kai domin yi wa yaransu allurar rigakafin domin hada hannu wajen yakar cutar.

Ya kuma ce a halin yanzu ma’aikatar ta karbi allurai fiye da miliyyan uku da dubu dari shida daga hukumar bunkasa lafiya ta kasa a matakin farko, inda ake sa ran yi wa yara miliyan uku da dubu dari biyu da arba’in da biyu da arba’in allurar, wadanda suke tsakanin watanni 59, inda kuma tuni aka baiwa ma’aikata dubu talatin horo a kan aikin.

Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan ya ce tuni ma’aikatar lafiya ta dauki matakan kariya cikin gaggawa domin hana cutar nan ta Corona Virus shigowa jihar Kano.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!