Labaran Kano
Al’umma su dinga riko da sana’o’i -KUST
Jami’ar Kimiyya da fasaha dake garin Wudil (KUST) ta bukaci al’ummar kasar nan da su yi riko da sana’oin noma da ta yadda hakan zai bunkasa tattalin arzikin kasar nan tare da rage rashin aikin yi ga matasa.
Daraktan sashin binciken aikin gona da dake kula da kwalejojin koyar da aikin gona dake karkashin jami’ar kimiyya da fasaha dake garin Wudil, Farfesa Abdu Muhammad Yero, ne ya bayyana hakan, yayin da yake zantawa da manema labarai kan nasarar da jami’ar ta yi na yaye matasa dari shida da suka fito daga jihar Kaduna wadanda suka koyi noma karkashin shirin bayar da tallafin noma na Appeals hadin guyiwa da sashin binciken aikin gona dake jami’ar ta Wudil.
Farfesa Abdu Muhammad Yero, ya kuma ja hankalin matasan da suka amfana da koyan aikin noman da su yi riko da abin da suka koya hannu biyu ta yadda zai amfane su tare da koyawa wasu da basu amfana da shirin ba.
Farfesa Abdu Muhammad Yero ya kuma godewa Gwamnatin tarayya da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da na jihar Kaduna Nasir El Rufai bisa yadda suke baiwa bankin duniya karkashin Appeal hadin kai wajen koyawa matasa sana’oin dogaro da kai.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya ruwaito cewa, an koyar da matasa dari shida yadda za su yi noman Citta da masara da alkama da Tumatur da kuma yadda zasu kiwata kaji da suka fito daga jihar ta Kaduna yadda za su dogara da kansu.