Coronavirus
A bi dokokin jami’an lafiya don kare yaduwar cutar Corona -Farfesa Musa Abdulkadir Tabari
An bukaci al’umma da su tabbatar da bin dokar malaman kiwon lafiya na daukan matakan kariya kan annobar Corona Virus.
Bukatar hakan ta fito ne ta bakin babban daraktan asibitin koyarwa dake Kaduna Barau Dikko, Farfesa Musa Abdulkadir Tabari a yayin zantawa da manema labarai
Farfesa Tabari ya ce akwai al’umma da ke ganin cewa cutar Corona ba gaskiya bane kirkirarrar cuta ce.
Ya kara da cewa duk da ba a samu bullar cutar a jahar Kaduna ba yana da kyau al’ummar jihar su dau matakan kariya ta hanyar kiyaye yawan taruwan da bai zama dole ba, da yawaita wanke hannu akai-akai domin gujewa kamuwa da cutar ta hanyar yin hannu da wani ko kuma ta hanyar taba wasu sassa irin su ido hanci ko kuma baki.
Babban daraktan ya kuma bayyana cewa ga duk wanda ya san ya halarci wata kasa ko jaha a nan Najeriya dake dauke da cutar covid19 ya tabbatar da ya killace kansa na mako biyu don tabbatar da cewa baya dauke da cutar, in kuwa ya ga alamomin cutar sun fara bayyana to ya hanzarta kai kansa asibiti mafi kusa.
Wakilinmu Haruna Ibrahim Idris ya ruwaito Farfesa Musa Abdulkadir Tabari ya bukaci al’umma da su guji tururuwa wajen zuwa asibiti don kuwa nan ne hanya mafi sauki da za a fi kamuwa da cutar
You must be logged in to post a comment Login