Connect with us

Labarai

Covid19: Shugaban sakatariyar kungiyar gwamnoni ya killace kansa

Published

on

Shugaban sakatariyar kungiyar gwamnonin kasar nan, Mr. Asishana Okauru ya killace kansa da dukkan nin iyalansa sakamakon zargin ko suna dauke da cutar Covid-19.

Mr Asishana Okauru ya ce, za ayi mishi gwaji shi da dukkan nin iyalan nasa domin sanin halin da suke ciki.

Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa wanda aka rabawa manema labarai a Abuja.

LABARAI MASU ALAKA

Da dumi-dumi: Ganduje ya baiwa ma’aikata hutu saboda Coronavirus

Da dumi-dumi Gwamnan jihar Bauchi ya kamu da COVID-19

Covid19: Osinbajo baya dauke da cutar

A cewar sanarwar, shugaban sakatariyar kungiyar gwamnonin ya dau wannan mataki ne biyo bayan ganawa da yayi da gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed a yayin taron kungiyar gwamnonin kasar nan da ya gabata.

A jiya talata ne dai aka bayyana gwamnan jihar ta Bauchi Bala Abdulkadir Muhammed a matsayin wanda ya kamu da cutar bayan gaisawa da ya yi da dan tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 333,104 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!