Connect with us

Labarai

A daren yau za mu saki sakamakon jarrabawar JAMB ta bana – Farfesa Ishaq Oloyede

Published

on

Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantun kasar nan JAMB ta ce a Larabar nan ne za ta fitar da sakamakon jarrabawar UTME ta bana.

Shugaban hukumar Farfesa Ishaq Oloyede ne ya sanar da hakan, yayin taron manema labarai a jihar Enugu.

Yana mai cewa hukumar ba ta da wata nufaka ko hujjar rike sakamakon matukar aka kammala tattarawa.

Farfesa Oloyede ya ce da zarar ya koma Abuja a yammacin yau din nan zai sahale a fitar da sakamakon jarrabawar.

“Mun tattara bayanan daliabai miliyan daya da dubu dari hudu da goma sha biyar, da dari biyar da daya ne suka yi rajistar jarrabawar ta UTME ta bana, inda mutane miliyan daya da da dubu dari da ashirin da biyu da casa’in da biyar kuma suka rubuta jarrabawar” in ji Farfesa Ishaq Oloyede.

Farfesa Ishaq Oloyede ya kuma ce dalibai dubu sittin da dari daya da goma sha daya ne ba su rubuta jarrabawar ba har yanzu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!