Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A karo na biyu lauyan Ibrahim Magu ya aike wa kwamitin bincike wasika

Published

on

A karo na biyu lauyan dakataccen shugaban hukumar yaki da cin hanci da rasha ta EFCC, Wahab Shittu ya rubuta  wasika ga shugaban  kwamitin da ke binciken tsohon shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Magu a kan  ya basu damar daukar bidiyon yanda binciken yake gudana.

Wahab Shittu ya bukaci shugaban kwamitin Ayo Salami da ya bayar da Tsofaffin kwafin bidiyon da aka fara dauka tun farkon binciken  domin nuna shi ga masoyan sa kafin daukar mataki na gaba.

Ta cikin wasikar Lauyan Ibrahim magu ya ce yin hakan bai sabawa kundin tsarin mulkin kasar nan ba karkashin sashi na talatin da shida ba.

A cewar Wahab Shittu kamata yayi kwamitin  ya ware rana guda  don baiwa Daktacen shugaban hukumar ta EFCC damar kare kansa a gaban Jama’a  domin suma su san halin da ake ciki.

A dai ranar Shida ga watan yuli ne Jami’an tsaro suka cafke dakatatten shugaban hukumar ta EFCC a gaban Offishinsa dake Abuja.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!