Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

A sanya Kalandar musulunci a manhajar karatu – Malam Mai Anwaru

Published

on

Limamin masallacin juma’a na Jami’ul Anwar da ke Tudun Yola Malam Abdulkadir Shehu Mai Anwaru ya yi kira ga gwamnati da ta sanya kalandar musulunci a manhajar karatu a makarantu.

Mai Anwaru ya bayyana hakan ne a wajen taron wa’azin sabuwar shekara da aka gudanar daren jiya Alhamis.

Ya ce, yana da kyau yara masu tasowa su san irin gwagwarmayar da sahabban manzon Allah A.S.W suka sha don tsara lissafin watannin musulunci.

Malam Abdulkadir Mai Anwaru ya kara da cewa, dukkanin halin da duniya da tsinci kan ta a ciki na fargaba na da nasaba da sabo ubangiji inda ya yi kira da al’umma da kuma masu ruwa da tsaki da su dage wajen yin addu’a don samun mafita.

Wasu daga cikin mahalarta taron wa’azin da suka zo daga kananan hukumonin jihar Kano sun bayyana yadda wa’azin ya kara musu karsashi musamman ta snin yadda sahabbai suka yi kokari na ganin an samar da kalandar musulunci.

Wakiliyar mu Madina Shehu Hausawa ta ruwaito cewa manyan malamai da dama ne suka halarci wa’azin, karo na uku wanda kuma za a shafe tsahon wata guda ana gudanar da shit un daga daya ga watan Muharram zuwa karshen watan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!