Labarai
A karon farko jirgin sama daga yankin Caribbean ya sauka a Najeriya

Wani jirgin kasuwanci na farko mai dauke da fasinjoji daga yankin Caribbean ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport, a wani sabon mataki na karfafa alakar tattalin arziki tsakanin kasashen yankin da nahiyar Afirka.
Jirgin wanda kamfanin Aquarian Consult Limited ya shirya, ya tashi daga Robert L. Bradshaw International Airport a ranar 21 ga watan Maris, 2026, dauke da sama da fasinjoji 100 da suka hada da ‘yan kasuwa, jami’an gwamnati da kuma fitattun ‘yan al’adu daga kasashe takwas na Caribbean, kafin saukarsa a Abuja a washegari.
Rahotanni sun ce wannan tafiya na daga cikin wani sabon salo na hulda kai tsaye tsakanin Caribbean da Afirka, ba tare da tsayawa a Turai ko Arewacin Amurka ba, wanda ake sa ran zai kara habaka kasuwanci da zuba jari tsakanin bangarorin biyu.
Haka kuma, wannan ci gaba na da alaka da taron zuba jari na Afirka da Caribbean da kamfanin Aquarian Consult ke shiryawa, wanda zai gudana a Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre daga ranar 23 zuwa 28 ga watan Maris, 2026.
You must be logged in to post a comment Login