Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

A karon farko Liverpool ta yi wa Manchester United ruwan kwallaye

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta yi nasarar lallasa Manchester United har gida da ci 5-0.

Karon farko cikin a tarihi da Liverpool ta taba yiwa Manchester United ruwan kwallaye.

Wasan da ya gudana a yau Lahadi 24 ga Oktoban 2021 da muke ciki a filin wasa na Old Trafford.

Wasan dai na hamayya ne da kungiyoyin suka buga tsakaninsu wanda jumulla ya zamana sun hadu sau 203.

Inda Manchester United ta yi nasara a wasanni
81 sai Liverpool ta yi nasara a wasanni 69 aka buga kunnnan doki sau 53.

Dan wasa Naby Keita ne ya zura kwallon farko a minti na 5, Sai kuma dan wasa Diago Jota ya zura ta biyu a minti na 15.

Kana Muhammad Salah ya zura kwallaye uku wato Hart rick a minti na 38 da 45 da kuma 50.

Sai dai a minti na 45 dan wasa Cristiano Ronaldo ya zura kwallo yayin da alkalin wasa ya soke sakamakon satar gida da ya yi.

Da wannan sakomako ya zamana Liverpool tana mataki na 2 da maki 21.

Yayin da Manchester United take a mataki na 7 da maki 14.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!