Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A rufe layin duk wanda bai hade shi da NIN ba – Buhari

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umarnin rufe layukan wayar da ba a hade su da lambar NIN ba.

Umarnin zai fara aiki daga yau Litinin 04 ga watan Afrilu na 2022.

A cewar shugaba Buhari ta bakin minisatan sadarwa da tattalin arziki na zamani Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya ce duk wanda bai hade layukansa na waya da lambar katin dan kasa ba ta NIN, zai rasa damar yin kiran waya a kowanne layi.

Ya ce, ya zuwa yanzu yan Najeriya sama da miliyan 125 ne suka hade layukansu da lambar NIN kamar yadda hukumar samar da lambar ta tabbatar.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!