Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An yankewa matashi hukuncin shakara 1 da kuma bulala sakamakon satar baburin Dan sahu

Published

on

Wata kotu a Kano ta yankewa wani matashi hukuncin dauri da bulala sakamakon samunsa da laifin satar baburin Adaidaita sahu.

Kotun shari’ar musulunci da ke zamanta a Fagge Yan Alluna Karkashin jagorancin Mai Sharia Dr. Bello Musa Khalid ta yankewa Aliyu Hussain hukuncin daurin shekara daya ko tarar Naira dubu Ashirin haka kuma za a tsalala masa bulala Talatin.

Tun da fari dai Lauyan gwamnati kuma mai gabatar da kara Barista Amra Uwais ita ce ta gabatar da wanda ake zarginsa da satar baburin Adaidaita na kimanin Naira dubu dari takwas.

Wanda ake zargin Aliyu Hussain ya amsa laifinsa nan take, hakan yasa yasa aka yanke masa hukuncin kamar yadda wakilin Freedom Radio Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!