Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A shirye Najeriya take a dama da ita tattalin arzikin Internet

Published

on

Ministan sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta internet Dr Isa Ali, Pantami ya ce, kasar nan a shirye take a dama da ita a  juyin juya hali a bangaren tattalin arziki na internet.

Ya kuma ce gwamnati a shirye ta ke ta yi aiki kafada da kafada da masana da ke jami’oi da sauran masu ruwa da tsaki wajen ganin an rika damawa da kasar nan a duk wata harka ta fasahar zamani.

Dr Isa Ali Fantami ya bayyana hakan ne yayin wani taro na kasa da kasa kan bunkasa fasahar sadarwa wanda aka gudanar ta kafar internet.

Haka zalika ministan ya kara da cewa daya daga cikin mataki na farko da gwamnati ta dauka don ganin ana damawa da kasar nan kan fasahar ta sadarwa shine sauya suna ma’aikatar daga ma’aikatar sadarwa zuwa ma’aikatar sadarwa da bunkasa tattalin arziki ta internet.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!