Connect with us

Labarai

Gwamnatoci ba su da iko kan titinan gwamnatin tarayya – Gbajabiamila

Published

on

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila ya ce ba abu ne mai yuwa ba, jihohin kasar nan su karbi jan ragamar kula da titina mallakin gwamnatin tarayya har sai an yi wa dokar da ta ba su iko gyaran fuska.

Femi Gbajabiamila ya bayyana hakan ne jim kadan bayan ganawa da gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun a birnin Abeokuta a jiya Laraba.

Shugaban majalisar wakilan wanda ya bayyana yadda lalacewar hanyar zuwa manyan masana’antu a jihar ya yi da abun takaici, yana mai cewar majalisar zata yi duk mai yuwa wajen an inganta hanyoyin jiha da samar da ababan more rayuwa.

Da yake bayani gwamnan jihar Dapo Abiodun y ace yana shawartar gwamnatin tarayya ta mallakawa jihohi wasu titina don samun saukin gyara su bayan da suka lalace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 330,179 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!