Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A yau ake sa ran shugaban Buhari zai gana da shugaban Amurka Donald Trump

Published

on

A yau Litinin ake sa-ran shugaban kasa Muhammadu Buhari zai gana da takwaransa na Amurka Donald Trump a birnin Washington DC, bayan amsa gayyatar Trump din da ya yi a jiya Lahadi.

Baya ga ganawar ta su da shugaba Trump, ana fatan zai tattauna da wasu kamfononin Amurka da saurn masu zuba jari domin ganin sun zuba jari a Najaeriya, a yunkurin da gwamnatin tarayya ke yi na farfado da tattalin arzikin kasa.

Tun a jiyan dai wasu ‘yan Najeriya da suka hadar da shugaban rukunin kamfanonin Dangote Aliko Dangote ya kai masa ziyara a masaukinsa.

Sauran da suka ziyarce shi sun hadar da shugabar kwamitin harkokin waje na majalisar Dattijai Sanat Monsurat Sunmonu da takwaranta na majalisar wakilai Nnenna Elendu Ukeji.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!