Connect with us

Labarai

Rashin nasarar yi wa Sanata Dino Melaye kiranye ba zai gurgunta siyasata ba-Gwamna Yahaya Bello

Published

on

Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya ce rashin nasarar yi wa Sanata Dino Melaye kiranye ba zai taba gurgunta masa siyasa ba, in ji mai magana da yawun gwamnan na Kogi Petra Onyegbule.

Yunkurin kiranyen na dan-majalisar Dattijan Kogi ta Yamma Sanata Dino Melaye ya gaza cimma nasara ne a ranar Asabar din da ta gabata bayan da kashi biyar ne kadai na masu kada kuri’a suka halarci kiranyen sbanin yadda doka ta bukaci har sai kashi 51 sun amince sannan kiranyen zai tabbata.

Masharhanta na ganin cewa kiranyen ya samu tasgaro sakamakon yadda gwamnatin Jihar ta Kogi ta ki biyan ma’aikata albashin wata-da-watanni, duk da cewa gwamna Yahaya Bello ya bayyana al’amarin a matsayin yunkurin kakkabe ma’aikatan bogi daga cikin ma’aikatan gwamnatin Jihar.

Dino Melaye ya zama dan-majalisar Wakilai a shekarar 2007 karkashin inuwar jam’iyyar PDP sai dai daga bisani ya sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki ta APC inda aka zabe shi a matsayin Sanata a shekarar 2015.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 340,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!