Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kasar Amurka ta yaba wa gwamnatin shugaba Buhari kan yaki da ta’addanci

Published

on

Kasar Amurka ta yabawa gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari, kan yakar ayyukan ta’addanci da take yi.

Shugaban kasar na Amurka Donald trump ne ya bayyana hakan, lokacin da yake jawabi yayin wani taron hadin gwiwa na manema labarai da shugabannin biyu suka gudanar a fadar white house ta Amurka.

Shugaba trump yace Najeriya itace kasa ta farko da ta fara bayar da goyon baya wajen yakar ‘yan tada kayar baya na ISIS.

Da yake nasa jawabi, shugaba Buhari ya bayyana jin dadin sa game da irin goyon bayan da Amurka take bawa Najeriya wajen yakar ‘yan tada kayar baya.

Shugaba Buhari ya kuma yabawa hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya, bisa irin goyon bayan da take bawa Najeriya, a bangaren kula da ‘yan gudun hijira, inda yace Amurka ce kan gaba daga cikin kasashen da suke tallafawa Najeriya a ayyukan jin kai.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kuma jaddada matakin gwamnatin sa na kokarin kwato daliba guda, daga cikin ‘yan matan sakandiren Dapchi da ta rage a hannun mayakan Boko Haram.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!