Labarai
Abba Kyari ya maka gwamnatin tarayya a gaban kotu
Dakataccen jami’in rundunar ƴan sandan nan da ke yaƙi da manyan laifukan a ƙasar nan DCP, Abba Kyari ya maka gwamnatin tarayya a gaban wata babbar kotun tarayya dake Abuja yana ƙalubalantar ci gaba da tsare shi da hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ke yi.
Cikin wata takarda mai lamba FHC/ABJ/CS/182/22 Kyari yana neman kotu ta gaggauta sakin shi.
Hakazalika DCP Abba Kyari wanda hukumar NDLEA ke tsare da shi ya ƙalubalanci zargin da NDLEA ke masa na yana da hannu a safarar miyagun kwayoyi, wanda ya bukaci kotu ta bada belinsa a cikin yanayi na sassauci.
Dakataccen jami’in ya shigar da ƙarar ne ta hannun lauyansa, Mrs P. O. Ikenna, da ke shaida wa kotun cewa ana tsare da shi a kan zargin ƙarya da aka yi masa.
Sai dai duk da haka, lokacin da aka gabatar da ƙarar, mai shari’a Inyang Ekwo, ya lura cewa ƙarar ta ƙunshi wasu abubuwan da za su buƙaci martanin gwamnatin tarayya.
Cikin ƙorafin da lauyan mai ƙara ya yi, ya buƙaci kotun da ta ba da umarnin a saki Kyari saboda rashin lafiyarsa.
A maimakon haka, sai mai shari’a Ekwo ya ba da umarnin a ba da dukkan matakan da suka dace a kan gwamanatin tarayya wanda aka bayyana shi a matsayin wanda ake ƙara shi kadai, kamar yadda ya dage ci gaba da sauraron ƙarar har zuwa ranar 24 ga watan Fabrairu.
You must be logged in to post a comment Login