Labarai
Abduljabbar ya sake musanta tuhume-tuhumen da ake masa
Yayin ci gaba da shari’ar zarge-zargen da ake yiwa Malam Abduljabbar Kabara a yau Alhamis 3 ga watan Maris na 2022, malamin ya rantse da al’ƙur’ani kan cewa bai aikata zarge-zargen da aka yi masa ba.
Tunda farko masu gabatar da ƙara ƙarƙashin Barista Suraj Sa’ida SAN sun gabatar da kansu, sannan suma lauyoyin malamin ƙarƙashin Barista A.O Muhammad suka gabatar da kansu.
A nan ne lauyan malamin ya buƙaci a bai wa wasu mutane da su shigo kotun domin taimaka masa wajen fitar da bayanai daga litattafai.
Nan dai aka yi ta tafka muhawara, daga ƙarshe malamin ya ce, a daina tababar zai yi komai da kansa, kotun kuma ta amince.
Daga nan aka tambayi Malamin ko zai rantse da alƙur’ani, ya amsa da eh, aka umarce shi da yayi alwala, ya ce, ai yana da alwala.
A nan ne mai shari’a ya umarci a ɗauko alƙur’ani ya miƙa wa malamin, inda ya rantse a kan zai faɗi gaskiya.
Nan take lauyansa ya fara da tambayarsa yana bada amsa, ciki kuwa har da tambayar ko ya amince da cajin da ake masa guda huɗu? Nan take ya ce bai aikata ba.
Ku ci gaba da bibiya domin jin yadda take kasancewa.
You must be logged in to post a comment Login