Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ina son a sauya mun kotu – Malam Abduljabbar Kabara

Published

on

Malam Abduljabbar Nasir Kabara ya bukaci a dauke shari’ar da ake yi masa daga gaban babbar kotun shari’ar musulunci zuwa wata.

Malamin ya bukaci hakan a zaman shari’ar na ranar Alhamis, karkashin jagorancin mai shari’a Ibrahim Sarki Yola, inda ya nuna rashin gamsuwarsa da yadda ake tafiyar da shari’ar.

Tun da fari dai kotun ta umarci Lauyan Malam Abduljabbar Kabara da ya dawo ya ci gaba da kare shi.

Sai dai mai gabatar da kara Barista Suraj Sa’ida (SAN) ya gabatar da lauyoyin dake dafa masa, bayan haka ne kuma kotun ta duba bangaren Lauyan malam Abduljabbar wato Barista Dalhatu Shehu amma bata ganshi ba.

Kotun ta kuma waiwayi bangaren wanda ake kara tunda kotu bata ga Lauyansa ba, tare da tanbayarsa ko yana da masaniyar rashin zuwan Lauyansa? malamin ya ce rashin zuwan lauyan nasa yana da alaka da takardar da ya rubuta zuwa ga alkalin alkalai na a canja masa kotu a mayar da shari’ar zuwa wata kotun.

Anan ne kotu ta tambaye shi ko me yasa? Sai yace saboda yana so a sami alkalin da bashi da wata alaka da bangarorin shari’ar.

Anan ma kotun ta tambaye shi ko zai iya fadar dalilan da yasa yace haka? sai ya ce akwai abubuwa da dama da yake ganin babu adalci, har ma yayi zargin cewa wani lokacin ana canja masa bayanansa haka kuma ya sake zargin lauyoyisa na farko a kan sun yi yunkurin mayar da shi mahaukaci lokacin da aka tambayeshi a gaban kotu suka hanashi magana.

Shi kuma Lauyan gwamnati ya fadawa kotu cewar bai kamata Lauyan Malam Abduljabbar yaki zuwa kotu ba, hakan yasa ba za su yi martani a kan abinda malamin ya fada ba.

Daga karshe kotun tace ai itace ta nada Lauyan Malam Abduljabbar kuma bisa doka babu wani mutum ko Lauya da zai zo da wata dabara ta dakatar da sharia.

Don haka kotu ta umarci Lauyan Malam Abduljabbar wato Barista Dalhatu Shehu yazo yaci gaba da aikinsa idan kuma ba zai zo ba, Malam Abduljabbar zai iya sake Lauya kafin ranar dawowa kotun.

Daga nan ne kuma kotun ta dage zaman zuwa ranar 28/7/22 domin sake gabatar da malamin, kamar yadda wakilin Freedom radio Aminu Abdu Bakanoma ya rawaito.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!