Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya fashe bai shafi makarantar da ke yankin ba -Gwamnatin Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ta tabbatar da cewa tukunyar Gas ɗin da ta fashe da safiyar yau Talata a unguwar Sabon Gari bai faru a wata makaranta ba.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Malam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce lamarin ya faru ne a wani kantin sayar da abincin dabbobi daura da makarantar da ke kan titin Aba a unguwar Sabon Gari a ƙaramar hukumar Fagge.

Yana mai cewa yayin da har yanzu ba a tantance musabbabin fashewar tukunyar Gas ɗin ba amma tuni an fara gudanar da bincike don gano musabbabin fashewar, da tasiri da kuma matakan da ya kamata a ɗauka.

Malam Garba ya yi kira ga al’ummar jihar musamman mazauna yankin da lamarin ya faru da su kwantar da hankalinsu domin kuwa gwamnati za ta sanar da jama’a kan duk wani ci gaba da aka samu tare da gargaɗin su da su daina yaɗa labaran da ba su da tushe.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!