Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tukunyar Gas ce ta fashe ba Bomb a – CP Dikko

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Kano ta ce tukunyar Gas ce ta fashe ta Bomb kamar yadda ake zargi.

Kwamishinan yan sandan Sama’ila Shu’aibu Dikko ne ya tabbatar da hakan ga wakilin Freedom Radio Abba Isah Muhammad.

Kwamishinan yayi bayanin ne lokacin da ya ziyarci wajen da lamarin ya faru jim kadan bayan fashewar tukunyar.

Sai dai ya tabbatar da cewa mutane 4 sun rasa ransu yayin da wasu da dama suka jikkata.

Kuma ya tabbatar da cewa an baza jami’an tsaro daban-daban a wajen don samar da tsaro ga al’umma.

A don haka ya bukaci al’ummar Kano su kwantar da hankalin su, domin kuwa ba Bom ne ya fashe ba kamar yadda ake ta yadawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!