Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya sanya Buhari ya gayyaci Ganduje da Shekarau

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gayyaci Gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da tsohon Gwamna Malam Shekarau domin ganawa da su kan shirin Shekaran na ficewa daga APC.

Wasu makusantan Malam Shekarau sun tabbatarwa da Freedom Radio hakan, jim kaɗan bayan da Gwamna Ganduje ya ziyarce shi a gidansa cikin daren yau.

A nasa ran jirgi zai tashi da su da misalin ƙarfe ɗaya na dare.

Wannan na zuwa ne bayan da Malam Shekarau ya kammala tattaunawa da magoya bayansa daga ƙananan hukumomin Kano arba’in da huɗu kan ficewa daga APC.

Labarai masu alaƙa

Shekarau ko Ganduje: Ina Gawuna ya ke?

Akwai yiwuwar Ganduje zai yi takarar Sanatan Kano ta Arewa

Rahotonni sun tabbatar da cewa magoya bayansa sun amince ya fice daga jam’iyyar APC zuwa NNPP ta tsohon Gwamna Kwankwaso.

Wani abu da ke daɗa tabbatar da hakan shi ne yadda magoya bayan nasa suka nuna rashin jin daɗi da zuwa Gwamna Ganduje gidansa a daren yau, yayin da Shekaran ke shirin bayyana matsayarsa a gobe Asabar.

Mai taimakawa Malam Shekarau kan kafafen sada zumunta Isma’il Lamiɗo ya wallafa a shafinsa na Facebook cewar.

“Malam zai amsa kira bisa girmamawa ta shugabanci! Zasu zauna da shugaban ƙasa a wannan dare da Gwamna Ganduje, Insha Allah wannan zaman ba zai canja komai a kan niyyar mu ta shiga NNPP ba”.

Ku kalli bidiyon ziyarar Ganduje gidan Shekarau

Malam Shekarau ya fara nuna shirin ficewa daga jam’iyyar ne tun bayan da kotun ƙoli ta tabbatar da shugabancin Abdullahi Abbas wanda ke tsagin Gwaman Ganduje.

A baya dai makusantan tsohon Gwamnan wanda ke neman takarar Sanata karo na biyu sun zargi cewa, tsagin Gwamnati na shirin yi musu ƙofar rago ta hanyar ganin an kayar da malamin a zaɓen fidda gwani.

Daga nan ne kuma Malam Shekarau ya fara zaman tuntuɓa da magoya bayansa a matakai daban-daban, har zuwa yau Jumu’a da rahotonni suka yi ƙarfi na cewa ya gama ɗaukar matsaya.

Da dai an shirya za a yi gangamin tarbar Malam Shekarau tare da tsohon Gwamna Kwankwaso yau daga Abuja amma hakan bai yiwu ba.

Tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau tare da tsohon gwamna Rabiu Musa Kwankwaso wani lokaci a baya.

Magoya bayan tsohon Gwamna Kwankwaso da sabbin ƴan jam’iyyar NNPP sun yi gangamin zuwa gidansa da ke unguwar Bompai a Kano, inda aka gabatar da jawaban siyasa.

Abin jira dai a gani shi ne zaɓin da Malam Shekarau zai ɗauka tsakanin matsayar magoya bayansa ko kuma ban bakin da Shugaba Buhari zai masa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!