Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abin da ya sanya muka hana jirage shawagi a Zamfara – Buhari

Published

on

Fadar shugaban kasa ta ce akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa akwai jiragen sama da suke jefa makamai ga ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ne ya bayyana haka yayin zantawa da jaridar Daily Trust.

‘‘Babu yadda za ayi gwamnati ta zura ido tana gani batagari suna amfani da jirage wajen tada tarzoma a kasar nan, wannan dalili ya sa gwamnati ta haramtawa jirage shawagi a sararin samaniyar jihar Zamfara’’ a cewar Malam Garba Shehu.

‘‘Mun samu labarai daga kafa mai karfi da ke cewa ana bani gishiri in baka manda tsakanin ‘yan bindiga da masu safarar makamai’’

‘‘Su bada makamai su kuma ‘yan bindiga su basu gwala-gwalai, inda masu safarar makaman ke jefawa ‘yan bindigar makamai ta sama’’ inji babban mataimaki na musamman ga shugaban kasar.

Idan za a iya tunawa a jiya ne gwamnatin tarayya ta sanar da haramtawa jiargen sama shawagi a sararin samaniyar jihar Zamfara da kuma hana masu hakar ma’adinai gudanar da aiki a jihar.

Mun hana jirage shawagi a sararin samaniyar jihar Zamfara ne saboda muna zargin jiragen suna jefawa ‘yan bindiga makamai inji Buhari.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!