Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abinda yasa ‘yan talla ke neman maganin tazarar haihuwa a Kano

Published

on

Abinda yasa ‘yan talla ke neman maganin tazarar haihuwa a Kano

Lamarin talla ga ‘ya’ya mata batu ne da ya zamo ruwan dare a manyan garuruwa da kuma kauyuka, ko a shekarar da ta gabata ma dai kungiyar Fulani ta Kano ta bukaci Fulani mata masu shigowa tallan Fura da Nono cikin gari da su dakata da kawo tallan bisa zargin wasu jama’a na yin lalata dasu.

Irin hakan ce ta faru a wannan makon da muke ciki, biyo bayan bullar wani bidiyo da yake nuna wasu ‘yan mata guda biyu masu talla a wani Asibiti da suke bayyana cewa sun zo ne domin a basu maganin tazarar haihuwa, kasancewar tallan da iyayensu ke dora musu basa samun wata riba ta azo gani, hakan yasa tilas su bada kansu ga mazaje mabukata domin samun gwagw-gwabar ribar da zasu kai wajen iyayensu domin suyi alfahari dasu.

Al’umma da dama dai suna ta bayyana mabam-mabamtan ra’ayi akan wannan batu a shafukan sada zumunta na zamani.

Hajiya Aishat Bello Mahmud wata mai fafutukar kare ‘yancin ‘ya’ya mata ce a nan jihar Kano, ta bayyana mana cewa suna iya kokarinsu wajen wayar da kan iyaye da al’umma baki daya kan illolin da yawon tallace-tallacen ke haifar musu, sai dai hakan bai iya magance matsalar ba, a don haka akwai bukatar gwamnati tayi doka mai tsauri kan tallace-tallace ga ‘ya’ya mata.

Ta kara da cewa an sha gwada masu tallace-tallacen a same su da cuta mai karya garkuwar jiki wato kanjamau.

 

Shin ko yaya kuke kallon wannan batu?

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!