Connect with us

Labarai

Abubakar Malami ya zargi EFCC da yin amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba

Published

on

Tsohon Ministan Shari’a na Najeriya Abubakar Malami, ya zargi hukumar EFCC da yin amfani da karfin iko ba bisa ka’ida ba, bayan da ya ce jami’an hukumar sun kwace gidaje da ofisoshinsa ba tare da umarnin kotu ba.

 

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Mohammed Bello Doka, ya fitar, Malami ya ce jami’an EFCC dauke da makamai sun mamaye kadarorinsa a safiyar Litinin, inda suka kama wasu mutane biyu. 

 

Ya kara da cewa umarnin kotu na wucin gadi da EFCC ke jingina da shi ya riga ya kare, domin an bayar da shi ne na kwanaki 14 kacal tun a watan Janairu.

 

Tun da farko dai, kotu ta bayar da umarnin wucin gadi na kwace kadarori 57 da ake zargin suna da alaka da shi da ‘ya’yansa, yayin da kuma yake fuskantar tuhume-tuhume daban-daban daga EFCC da DSS

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!