Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta bai wa EFCC damar ci gaba da tsare Godwin Emefiele

Published

on

Babbar kotu a Ikeja da ke birnin Lagos, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya CBN, Godwin Emefiele.

Kotun, ta bai wa hukumar EFCC damar ci gaba da tsare Mista Godwin Emefiele  har zuwa ranar 11 ga watan nan da muke ciki na Afrilu da za ta yanke hukunci kan yiwuwar bayar da shi beli.

Yayin zaman kotun dai, tsohon gwamnan babban bankin, ya musanta sababbin tuhume-tuhumen da ake masa na karya dokokin da suka shafi hada-hadar kuɗaɗen kasashen waje da hukumar EFCC ke masa.

BBC ta ruwaito cewa, hukumar EFCC ta zargi Godwin Emefiele da ware wasu kuɗaɗen waje kusan Dala biliyan biyu ba tare da bin ka’ida ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!