Labarai
Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ware kowa ce ranar alhamis ta mako na biyu a watan Oktoba a matsayin ranar gani ta duniya da nufin wayar dakan al’umma kan matsalar gani da yadda ya kamata su kare kansu daga cutuka da ka iya jawo cutar makanta.
Kazalika ranar tana maida hankali ne kan yadda za a taimakawa masu lalurar gani acikin al’umma.
Wakilin mu Aminu Ibrahim Abdullahi ya gana da kwararran likitan lafiyar Idanu na Asibitin Aminu Dr, Sadiq Hassan kan muhimmancin wannan ranar.