Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abubuwan da ke haifar da cutar suga: Dr Gezawa

Published

on

Shirin barka da hantsi

Wani likitan masu fama da cukar sukari ya bayyana cewa karancin sinadarin da ke taimakawa jikin dan Adam wajen samar da ingantaccen suga a jiki na daya daga abinda ke haifar da cutar a jikin dan Adam.

Dr Ibrahim Danjummai Gezawa ,likitan masu fama da cutar sukari a asibitin koyarwa na malam Aminu dake Kano ne ya bayyana hakan bayan kammala shirin barka da hantsi na nan tashar freedom radiyo da ya mayar da hankali kan bikin ranar masu fama da lalurar da yake gudana a yau.

Ya kara da cewa, yawan shan ruwa da bushewar makogwaro da yawan fitsari tare da sagewar wani sashi na jiki na daya daga cikin alamomin cutar suga a jikin dan Adam.

Dr Ibrahim Danjuma Gezawa yace cin abinci ko abin sha mai karancin sukari tare da yin amfani da ganyayyaki a cikin abinci na taka rawa wajen samar da lafiya a jikin mai fama da cutar, inda yace wani bincike da suka gudanar ya nuna cewar a kowanne sakan ashirin ana yankewa mutum guda kafa sakamakon cutar sikari.

Abdulkarim Sale daya daga cikin masu fama da cutar suga tsawon shekaru shida ya bayyana halin da ya samu kan sa tare kuma da matakan da ya bi wajen kiyaye ka’idojin da aka gindaya masa.

Ya ce da farko ya fuskanci matsaloli na zazzabi, yawan jin kishirwa, rama da yawan gajiya.

Ya kara da cewar yana fari jin wadannan alamu sai ya garzaya asibiti inda liita ya rubuta masa magani tare da bashi shawarwari na irin na’oikan abincin da ya kamata ya ci, matso jiki da sauran abubuwan da zai kare kansa.

Abdulkarim Sale ya yi kira ga masu fama da cutar sukari da su rika neman shawarwarin masana harkar lafiya a koyaushe musamman ma idan suka ji sauyin yanayi a jikin su.

Taken ranar ciwon sukari na duniya dai a bana shine -ciwon suga da iyali’ wanda yake Magana kan yadda iyali zasu taimakawa mai lalurar ciwon suga , yadda zasu kula da kansu da irin nau’ikan abincin da zasu ci.

Sannan ranar na nuni ga yadda al’umma zasu gani alamomin lalurar ciwon suga.

An dai fara gudanar da ranar ciwon suga ne a 1991 biyo bayan yawaitar masu dauke da ciwon suga da bukatar wayar da kan al’umma dangane da alamomi da yadda z’a kare kai daga kamuwa da ciwon.

Majalisar dinkin duniya ce ta ware wannan rana a shekara ta 2006 tun daga wannan shekara ne ake gudanar da ranar a duk duniya.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!